Al'umar Ghana na zaben sabon shugaban kasa da 'yan majalisu

Bayanan bidiyo,

Rahoton Ibrahim Isa kan yadda zaben da kuma harkoki ke gudana

Jama'a a Ghana sun fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa inda masu sharhi ke cewa fafatawa za ta yi zafi tsakanin John Mahama da fitaccen jagoran adawa Nana Akufo Addo.

Duka 'yan takara bakwai na zaben sun yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya.

Sai dai wani magoyin bayan 'yan adawa ya rasa ransa a lokacin wata tarzoma da ta biyo bayan yakin neman zabe.

Batun tabarbarewar tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa su ne suka mamaye yakin neman zaben.

Ana sa ran samun sakamakon zaben cikin kwanaki uku.

Za a gudanar da zagaye na biyu nan gaba a wannan watan idan babu wanda ya samu fiye da kashi 50% a cikin manyan 'yan takarar biyu.

Bayanan hoto,

An tsaurara matakan tsaro a wuraren kada kuri'a

Ba dai wannan ne karo na farko da Nana Akufo-Addo mai shekara 72 ke tsayawa takarar shugabancin kasar ba, karo na uku kenan da yake neman kujerar.

Masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin cewa idan har ya sha kaye a wannan karo, to hakan zai kawo karshen damawa da ake yi da shi a siyasar kasar saboda shekarunsa.

A bangare guda kuma idan har Shugaba Mahama ya fadi zaben, to shi ne zai zamo shugaban kasar na farko da ya yi wa'adin mulki sau daya a tarihin dimukradiyyar Ghana.

Idan kuma ya yi nasara, zai kafa tarihin zama shugaba na farko na farar hula da ya dade ya na mulki tun bayan da Ghana ta fara amfani da jam'iyyun siyasa daban-daban.

Saboda shi ne ya karashe sauran wa'adin mulkin marigayi John Atta Mills da ya rasu a shekarar 2012.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu sharhi na ganin fafatwa za ta yi zafi tsakanin John Mahama da fitaccen jagoran adawa Nana Akufo Addo

Bayanan hoto,

Tun cikin dare wasu mutanen suka kama layi ta hanyar ajiye duwatsu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana sa ran samun sakamakon zaben cikin kwanaki uku