'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a Brazil

Masu zanga-zanga sun kafa shingaye a wajen ginin Majalisar dokoki a birnin Rio

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga sun kafa shingaye a wajen ginin Majalisar dokoki a birnin Rio

Jami'an 'yan sanda a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashen roba wajen tarwatsa masu zanga-zanga dake nuna rashin jin dadin su akan matakin tsuke bakin aljihu.

Akasarin masu zanga zangar dai ma'aikatan gwamnati ne wadanda suka mamaye harabar majalisar dokokin jihar dake tsakiyar birnin.

Hotunan talbijin da aka watsa sun nuna 'yan sanda na harba harsashen roba akan masu zanga-zanga daga wasu tagogin wani coci.

Tuni dai hukumomin cocin na Roman Catholika suka ce zasu gudanar da bincike.