2016: Ana zaben kasar Ghana

Magoya bayan jam'iyyun siyasar Ghana
Bayanan hoto,

Magoya bayan 'yan takarar sun shirya tsaf, dan fara kada kuri'a

A ranar laraba ne ake zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar Ghana.

Shekaru 25 kenan da kasar Ghana ta koma turbar mulkin Dimukradiyya, kuma wannan shi ne karo na bakwai da al'umar kasar za su kada kuri'ar zaben shugaban kasa.

A wannan zaben dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC da Nana Akufo-Addo na jam'iyyar NPP.

Akwai kuma wasu 'yan takarar da za su wakilci jam'iyyu hudu, da kuma indifanda.

Ba dai wannan ne karo na farko da Nana Akufo-Addo mai shekara 72 ke tsayawa takarar shugabancin kasar, karo na uku kenan da yake neman kujerar.

Masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin cewa idan har ya sha kaye a wannan karo, to hakan zai kawo karshen damawa da ake yi da shi a siyasar kasar saboda shekarunsa.

A bangare guda kuma idan har Shugaba Mahama ya fadi zaben, to shi ne zai zamo shugaban Ghana na farko da ya yi wa'adin mulki sau daya a tarihin dimukradiyyar kasar.

Idan kuma ya yi nasara, zai kafa tarihin zama shugaba na farko farar hula da ya dade ya na mulki a kasar tun bayan da Ghana ta zamo mai jam'iyyun siyasa daban-daban.

Saboda shi ne ya karashe sauran wa'adin mulkin marigayi John Atta Mills da ya rasu a shekarar 2012.