Mutane 24 sun mutu a girgizar kasa a Indonesia

Girgizar kasa a Indonesia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da kasar ke fuskantar girgizar kasa ba

Akalla mutane 24 suka mutu a wani mummunar girgizar kasa data abku a lardin Ace dake arewacin Indonisiya.

Wani jami'i a yankin ya ce akwai mutane da dama da ake kyautata zaton sun makale a baraguzan gidajen da suka ruguje.

Girgizar kasar data kai maki 6 da digo 4 ta abkawa yankin dake gabar teku ne da sanyin safiya.

Wasu hotunan talbijin sun nuna masallatai da gidaje da wasu wuraren sun yi kaca-kaca a garin Pidie Jaya.

A shekarar 2004 al'ummar lardin Aceh sun fuskanci mummunar girgizar kasa da guguwar tsunami ta haddasa data kwashe wasu kauyukan dake gabar tekun India.