Me ya sa babu bayanan mata da dama a shafin wikipedia?

Amina Mohammed

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Amina Mohammed ta taka rawar gani a fannoni da dama na rayuwa

WikiProject wani bangare ne na shirin BBC na mata 100 rabin muryar al'umma da ke da nufin kara yawan mata da ke da bayanan irin rawar da suka taka a al'umominsu a kan shafin intanet na wikipedia.

A ranar Alhamis ne za mu wallafa bayanan mata da dama wadanda suka taka muhimmiyar rawar gani a Najeriya a shafin na Wikipedia.

Wasu daga cikin matan sun hada da:

Hajiya Amina Mohammed: Ita ce ministar muhalli ta Najeria wacce aka nada a ranar 11 ga watan Nuwambar shekarar bara.

Amina ta taka muhimmiyar rawa wajen ayyana matakan cigaban al'umma lokacin tana mai bada shawara ta musamman ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon a kan matakan cigaban al'umma a 2015.

Aloma Mariam Mukhtar: Na daya daga cikin matan da za mu saka bayananta a shafin na Wikipedia. An haife ta ne a ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 1944.

Aloma ta zamo mace ta farko a fagen rayuwa da dama a Najeriya.

Ita ce mace lauya ta farko a arewacin Najeriya kuma mai shari'a mace ta farko a babbar kotun jiha da ke Kano a arewacin kasar.

Baya ga haka ita ce mace mai shari'a ta farko a kotun daukaka kara ta Najeriya.

Aloma ta kuma kasance mace ta farko mai shari'a a kotun kolin Najeriya sannan kuma mace ta farko da ta yi aikin a matsayin babbar jojin Najeriya.

Bayanan hoto,

Hajiya Hafsat Abdulwaheed ta rubuta littattafai fiye da 30

Hafsat Abdulwaheed: Na daya daga cikin matan da suka taka muhimmiyar rawar gani a Najeriya amma kuma babu bayananta a shafin wikipedia.

A don haka tana daya daga cikin matan da za mu wallafa bayannanta a shafin.

Hafsat Abdulwaheed tana rubutun zube da wakoki kuma ita ce mace ta farko da aka wallafa littafinta na kagagen labari a harshen Hausa.

Hafsat ta taba yunkurin tsayawa takarar gwamna a jihar Zamfara a shekarun 2000.

Za ku iya kasancewa tare da mu kai tsaye a shafinmu na Facebook daga karfe 11 na safe a ranar Alhamis domin ganin yadda za mu tafiyar da aikin WikiProject inda za mu kara bayannan wadannan matan da wasu daban wadanda suka cancanta a kara bayanansu.