Leipzig: Ba ma bukatar Ronaldo ko Messi

RB Leipzig

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Leipzig ce kungiya ta farko daga tsohuwar Jamus ta Gabas da ta zama ta daya a Bundesliga tun bayan Hansa Rostock a 1991

Gagarumin cigaba da bunkasa da kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig ta yi daga kananan lig-lig har ta je babbar gasar Jamus ta Bundesliga sun ba wa masu sha'awar wasan kwallon kafa mamaki a fadin Turai.

To amma wani abin mamaki shi ne, yayin da kungiyoyin kwallon kafa a duniya musamman Turai ke burin daukar gwanayen 'yan wasa kamar Cristiano Ronaldo da Lionel Messi, su kam sun ce ba sa bukatar gwarzayen.

Darektan kungiyar na wasanni ya ce ko alama ba za su taba daukar tsoffin 'yan wasa kamar su Ronaldo ko Messi ba.

Domin duk da kwarewarsu da sunan da suka yi, ba dabara ba ce a tsarin kasuwancin wasa ka sayi irinsu, domin sun doshi shekara 30 ko fin haka.

Ita kuwa kungiyar a yanzu 'yan wasan da ta dauka kafin gasar bana dukkaninsu za ka ga 'yan shekara 19 zuwa 20 ko 21, domin tana so ta kasance da matasan 'yan wasa.

Sai dai kallon da ake musu yanzu shi ne, ko za su yi irin ta Leicester su ma su zama zakarun gasar Bundesliga ta Jamus?

Ana ganin hakan ka iya kasancewa domin su ne na daya a tebur yanzu da maki 33 a wasa 13, Bayern Munich na binsu da maki 30.

Kuma ga shi suna da kudi da kwararru da duk goyon bayan da suke bukata, domin duk da 'yan matsalolin da suka faro gasar bana da su, magoya bayansu na cika fili idan za su yi wasa.

Wannan ne ma ya sa a yanzu har suke tunanin gina wani sabon babban filin wasa.