Za a rika bayar da jan kati a wasan kurket
Australia's Glenn McGrath was jokingly shown a red card by umpire Billy Bowden

Asalin hoton, Getty Images
Alkalin wasan kurket Billy Bowden na barkwancin ba wa Glenn McGrath na Australia jan kati a gasar farko ta Twenty20 a 2005
Za a bullo da tsarin bayar da jan kati wanda alkalin wasa ke korar dan wasa idan ya aikata wani babban laifi, a wasan kurket, kamar yadda ake yi a kwallon kafa
Za a fara sabon tsarin ne a wasan a karon farko a shekara mai zuwa, haka kuma za a rika takaita girman muciyar dukan kwallon daga lokacin.
Dan kwamitin hukumar kula da wasan na Kurket ta duniya Ricky Ponting, ya bayyana cewa za a yi hakan ne domin rage aikata manyan laifuka a wasan.
Tsohon kyaftin din na Australia ya ce an yanke shawarar yin hakan ne domin wasu 'yan wasan na neman wuce gona da iri.