Za a yiwa matar da tafi sauran mata teba a duniya tiyata

Eman Ahmed Abd El Aty ta shafe shekaru 25 ba ta fita ko kofar gida ba
Bayanan hoto,

Eman Ahmed Abd El Aty ta shafe shekaru 25 ba ta fita ko kofar gida ba

Za a kai matar da akayi amanna tafi sauran matan duniya teba da nauyinta ya kai kilogiram dari biyar a kasar India domin ayi mata tiyatar rage kiba.

Eman Ahmed Abd El Aty, 'yar asalin kasar Masar mai kimanin shekaru talatin da shida, za a kaita a cikin wani jirgi da akayi shata inda Dr Muffazal Lakdawala zai mata tiyatar rage kibar.

Da farko ofishin jakadancin India da ke Masar ya ki amincewa da yi mata takardar izinin shiga kasar ta India wato visa saboda ba zata iya zuwa da kanta ba.

To amma bayan likitan da zai mata aikin ya turawa ministar harkokin wajen India sako ta Twitter, sai komai ya canja aka amince da bata visa.

Iyalan Wannan mata mai kiba sun ce ta shafe shekaru ashirin da biyar ba ta fita ko kofar gida ba.

Idan dai har aka tabbatar da nauyin nata ya kai kilogiram dari biyar, to zata kasance macen da ta fi dukkan matan duniya nauyi da ke raye, kuma hakan zai bata damar shiga cikin kundin tattara abubuwan bajinta na Guiness, bayan Pauline Potter 'yar kasar Amurka wadda ta shiga kundin a shekarar 2010, inda nauyinta ya kai kilogram 292.