Matar da ta haifi jikanta da kanta

Julie Bradford, da diyarta diyarta Jessica Jenkins

Asalin hoton, Wales News Service

Bayanan hoto,

Julie Bradford, ta haifi jikanta da kanta, saboda cutar sankarar da ta yi sanadin lalacewar mahaifar 'yarta

Wata mata ta haifi jikanta da kanta, bayan da ta bai wa diyarta aron mahaifa.

Julie Bradford, mai shekara 45, ta haifar wa diyarta, Jessica Jenkins, jariri mai suna Jack ne, saboda mahaifar 'yar ta lalace sanadiyyar magungunan cutar sankara, wato cancer, da ta ke sha.

Jessica mai shekara 21, da ke zaune a garin Rhymney, ta adana kwayayenta ne a cikin kankara a asibitin Cardiff da ke Wales, kafin ta soma shan magungunan cutar da ta ke fama da ita, wanda ta soma shekaru uku da suka gabata.

Jessica ta ce an haifi Jack a Juma'ar da ta gabata, kuma cikin koshin lafiya.

Ta ce, "Mahaifiyata ta nuna bajinta, kuma babu wanda ya kai ta kima a duniya a wajena. Ina matukar kaunar ta, saboda ita ta ba ni da na."

Ta kara da cewa, "Tun lokacin da nake karama nake fatan na ga na zama uwa, kuma wannan mafarki nawa ya zama gaskiya."

Jessica da mijinta sun yanke shawarar amfani da tsarin dashen kwan mai suna IVF ne a farkon wannan shekarar, bayan ta samu sauki daga cutar a 2014.