Indonesia: Girgizar kasa ta kashe mutum kusan 100

Asalin hoton, AP/GETTY IMAGES
Masallatai da gine-gine da dama sun ruguje
Ma'aikatan agaji a lardin Aceh na arewacin Indonesia na ci gaba da laluben wadanda suka tsira bayan wata gagarumar girgizar kasar da ta kashe mutane kusan 100.
Hukumomin Indonesia sun ce girgizar kasar mai karfin maki 6.5, ya afku ne kusa da tsibirin Sumatra da ke arewa maso gabashin kasar, kuma ta lalata daruruwan gine-gine, inda hotunan talabijan suka nuna gine-ginen masallatai da gidaje sun ruguje baki daya a gundumar Pidie Jaya.
Lardin Aceh dai ya yi fama da mummunar barna, a shekara ta dubu biyu da hudu, lokacin da girgizar kasa mai karfin maki tara da digo biyu ta haddasa igiyar ruwan Tsunami, wadda ta shafe daukacin al'umomi dake kewayen tekun India.
Musman Aziz, wani mazaunin Meureudu, daya daga cikin garuruwan da lamarin ya shafa, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AP cewa, "Gaskia lamarin ya munana, girgizar kamar ta ma fi wanda aka yi a shekarar 2004...na tsorata matuka, sai na ji kamar za a kuma yin Tsunami."
Kasar Indonesiya dai na fuskantar hadari girgizar kasa saboda kusancin ta da zagayen wani yanki da aka yi wa lakabi da 'Ring of Fire'- wani yanki da ke zagaye da yawaitar samun aman wuta da girgizar kasa a yankin Pacific.
Tsibirin na Sumatra ya sha fama da girgizar kasa a wannan shekarar.