Nigeria: An gurfanar da wasu jami'an gwamnatin Kano a kotu

Tambarin kotu a Kano Nigeria

Asalin hoton, AFP

Hukumar karbar koke-koke da yaki da cin hanci ta jihar Kano a Nijeriya ta gurfanar da kwamishinan k'asa da tsare-tsare na jihar a gaban kotu kan zargin karkatar da filayen mutane.

Ana zargin Kwamishinan Faruk BB Faruk da wani tsohon Babban Sakatare a ma'aikatar, Mahmud Bello Bari da wani darakta, Ahmad Ibrahim da laifin cin amana da kuma sayar da fulotan mutane.

Duka mutanen uku sun musanta wannan laifi da ake zarginsu da aikata wa.

Mai gabatar da k'ara, Barista Rabi Ibrahim Waya ta ce laifukan sun saba da sashe na 97 da na 315, kafin daga bisani alkalin babbar kotun Nasir Saminu ya bayar da belin kwamishinan tare da dage shari'ar zuwa ranakun 17 da 18 ga watan Janairu.

Kano na daga cikin manyan birane a Najeriya da ke fama da badakala da harkallar filaye.

Wannan ne ma ya sa mutane ke zagaye fulotansu suna rubuta "Ba na sayarwa ba ne" don ankaraswa.