Nigeria: 'Dalilin da ya sa aka kai hari Madagali'

Taswirar Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun fara hasashen dalilin kai harin bam a Madagali ta jihar Adamawa ranar Juma'a, inda mutum akalla 45 suka mutu sannan wasu 33 suka jikkata.

Wasu mata ne dai ake tsammanin sun tayar da tagwayen bama-baman a kasuwar garin na Madagali.

Hukumar Agajin ta NEMA ta ce yanzu haka wadanda suka jikkata suna asibitoci daban-daban domin samun kulawa ta musamman.

Mudassir Bello, jami'in hukumar ta NEMA a jihohin Adamawa da Taraba, ya ce, kusancin garin na Madagali da dajin Sambisa da kuma nisan da jami'an tsaro suka yi nesa da garin ne ya sa sa mahara suka kai harin.

Sai dai kuma har yanzu babu wadanda suka dauki alhakin kai harin.

Sai dai kungiyar Boko Haram wadda ta yi shekara bakwai tana yakar gwamnatin kasar ta dade tana kai harin bama-bamai a yankin.

Wasu gwamman mutane sun samu raunuka, kamar yadda mai magana da yawun soji a yankin Manjo Badare Akintoye ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Har yanzu babu wadanda suka dauki alhakin kai harin

Maharan guda biyu, wadanda suka yi bazata a matsayin masu sayayya, sun tayar da bam din ne a wani bangare na wata kasuwa da ake sayar da kayan gwanjo.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nema ta ce masu aikin ceto da bayar da agaji sun isa wurin.

Boko Haram ta mamaye garin Madagali na tsawon watanni har zuwa bara lokacin da sojojin Najeriya suka fatattake su.