Yawan matan da ke wasanni ya kai yadda bai taba kaiwa ba

'Yan mata Musulmi na kwallon hannu

Asalin hoton, Mehr

Bayanan hoto,

Wasu mata Musulmi na wasan kwallon hannu da dan kwali

Yawan matan da ke wasanni akai akai a duniya ya kai yawan da bai taba kaiwa ba zuwa miliyan bakwai da dubu dari biyu da goma kamar yadda wani bincike ya nuna.

Binciken na kungiyar Sport England, ya gano cewa yawan matan da suke shiga wasanni ya karu da 250,000 tun lokacin da kungiyar ta kaddamar da shirinta na wayar da kan mata su rika shiga wasanni (This Girl Can) a 2014.

Bambancin yawan maza da matan da suke wasanni ya ragu kamar yadda nazarin ya nuna zuwa miliyan daya da dubu dari biyar da hamsin.

Haka kuma gaba daya an samu karin mutanen da ke wasanni akai akai maza da mata har 229,400, idan aka kwatanta da shekarar da ta wuce.

Shugaban kungiyar ta Sport England Jennie Price ya ce: Wadannan alkaluma suna karfafa guiwa, musamman karin yawan matan da suke wasa da kuma motsa jiki a kowane mako.

Ya ce, ''shirinmu na wayar da kan mata su rika shiga wasanni domin magance bambancin da ake da shi tsakanin maza da mata a wasanni yana samun nasara a shekara biyu kawai da kirkiso shi.

Duk da wannan nasara ta samun karin mata da ke shiga wasanni daban-daban, binciken ya nuna cewa an samu raguwar mata a wasanni biyu, wadanda a da suke bunkasa sosai.

Wasannin biyu da ke samun raguwar su ne na guje-guje da tsalle-tsalle da kuma tseren keke.