Mata 100: Yadda muke tallata bajintar mata —Gbemi

Mata da dama na kago abubuwan ci gaban al'umma amma ba kasafai a kan ji labarinsu ba.Wannan ne ya sa wata matashiya wadda ita ma ta kan kago abubuwa, musamman a intanet, ta yanke shawarar samar da wani dandali wanda zai rika zakulo mata masu fasaha yana kuma tallata abubuwan da suka yi.

Gbemi Adekanbi

Asalin hoton, Gbemi Adekanbi

Bayanan hoto,

Gbemi Adekanbi ta ce burinta shi ne tallata bajintar da mata ke yi

Suna na Gbemi Adekambi, ina gudanar da wani shafin intanet mai suna ForCreativeGirls ni da kawata Chioma. Shafin yana zakulo mata masu fasaha yana kuma ba da labarinsu da buda musu hanyoyin da za su samu ci gaba cikin harkokinsu.

Kusan shekara biyu ke nan yanzu da shiga ta harkar kago abubuwa a intanet. Wata rana ina zaune sai na ke cewa mata fa sun dade suna kirkirar wasu abubuwa na bajinta amma ba a jin labarinsu. Sai na ce to me zai hana - mu ma mayar da hankali a kan harkokin da mata su ke gudanarwa mu kuma ba da labari a kan ayyukan da suke yi ?

Mata na ayyuka na ban mamaki; me zai hana mu samar da wani dandali da za a rika bayar da labarinsu saboda hakan ya zaburar da wasu matan su bi sahunsu, wasu kuma su ga abin da suka yi?

Yanzu haka muna duba yiwuwar gudanar da wani taro a badi, inda za mu gayyato matan da su ka yi fice a fannonin da suka kware domin su ba da horo ga mata masu tasowa.

In ka shiga shafinmu na intanet za ka ga hirarrakin da muka yi da mata kimanin casa'in. Wannan wani aiki ne mai yawa. Da yawa daga cikin matan da ke kago abubuwan ci gaba na fuskantar matsalar yayata abin da suke yi saboda jama'a su gani. To idan ka je shafin za ka ga ayyukan da matan suke yi da kuma bayani a kan yadda za ka tuntube su. Shafin wani dandali ne da ake baje kolin irin fasahar da Allah Ya yi wa mata kuma yana nuni da cewa duk abin da muka za zuciyarmu a kan za yi, to za mu iya. Na ga ayyukan da wasu mata suka yi wadanda suka tafi da imani na. Abin da hakan ke nufi shi ne duk wani abu da ki ka kwallafa ran ki a kansa, sannan kika nemi a tallafa mi ki, to lalle hakar ki za ta cimma ruwa.

Asalin hoton, Gbemi Adekanmbi

Bayanan hoto,

A shafin For Creative Girls akwai hira da bayanan mata akalla 90