An kashe 'mutum 11' a tarzomar da ta barke a Kamaru

Hakin na tashi a asibitin Bamenda

Asalin hoton, Whatsapp/Bamenda Resident

Bayanan hoto,

An yi zargin 'yan sanda sun yi amfani harsashai na gaske kan fararen hula a Kamaru

Ana ci gaba da zaman dar-dar a garin Bamenda na Kamaru bayan da mutum 11 suka mutu a tarztarzomar da ta barke tsakanin matasa da jami'an tsaro a Arewa maso Yammacin kasar.

Wadanda suka shaida lamarin, wanda ya faru a ranar Alhamis da yamma, sun ce jami'an tsaro sun yi amfani da harsashe masu kisa wajen tarwatsa zanga-zangar da a cewarsu, ta lumana ce.

Mazauna birnin Bamenda sun yi ta watsa hotunan tarzomar a shafin zumunta na Whatsapp.

Wani Lauya a birnin ya shaida wa BBC cewa, ba zai iya komawa gida daga wurin aiki ba, saboda jami'an tsaro na amfani da harsashen gaske wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

Harmony Bobga, daga kungiyar lauyoyin Kamaru, na daya daga cikin lauyoyin da ke jagorantar fafutukar da ake yi na yaki da dokar da aka kafe ta cewa dole a yi amfani da harshen Faransanci a yankunan da ake yin Turanci a kasar.

Ya ce ya yi magana da wasu da lamarin ya afku a gabansu, a wani babban asibiti da ke birnin, inda suka shaida masa cewa fararen hula shida da wani dan jami'iyya daya da kuma 'yan sanda hudu sun mutu.

Tarzomar ta barke a yayin da jam'iyya mai mulki ta soma gudanar da wani taron siyasa a Bamenda.

Mista Bobga ya ce sun samu rahotanni cewa Firayi Ministan Kamaru, Philemon Yang, wanda shi ya kamata ya jagoranci taron siyasar, ya boye a wani otal mai suna Abaya, a inda jami'an tsaro suka tsaurar tsaro.