Syria: 'Yan tawaye sun yi kira da a dakatar da yaki

Al'ummar birnin Aleppo da ke Syria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan tawaye sun yi kira da a dakatar da yaki domin fararen hula su samu kulawa

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergie Lavrov, ya ce rundunar sojin Syria ta dakatar da kai hare-hare a gabashin Aleppo domin bayar da damar kwashe dubban fararen hula dake zauna a yankin dake hannun 'yan-tawaye.

Mista Lavrov ya ce yana shaida wa duniya a yau cewa, rundunar sojin Syria ta dakatar da daukar matakin soji gadan-gadan a gabashin Aleppo.

Ya kuma kara da cewa an yi hakan ne saboda yanzu haka ana gudanar da aiki mafi girma, na kwashe fararen hula dake son ficewa daga gabashin Aleppo.

Da yake magana a gefen taron kolin ministocin harkokin waje na kasashen Turai, Mr Lavrov ya kara da cewa Rasha na da aniyar gamawa da abinda ya kira sauran 'yan ta'adda dake Syria.

Ya ce kwararrun soji na Rasha da Amurka zasu gana a Geneva ranar Asabar domin tattauna halin da ake ciki a Aleppo.