'Kora daga aiki ta sa na rungumi tukin keke

Yana da sakamako mai kyau na babbar Diploma
Image caption Onovo Ugochukwu bai yi girman kai ba

Onovo Ugochukwu, matashi ne dan jihar Enugu a kudancin Najeriya wanda ya rungumi sana'ar tuka 'keke Napep' domin samun na sa wa a bakin salati.

A baya dai, Onovo ya kasance ma'aikacin wani kamfanin robobi.

Sai dai sakamakon matsin tattalin arzikin da Najeriya ta ke fuskanta, kamfanin ya kore Onovo da wasu abokan aikinsa.

To amma saboda karfin hali da son neman halak, Ugochukwu ya ajiye matakin karatunsa na babbar Diploma, a inda kuma ya rungumi sana'ar tukin 'keke Napep'.

Image caption Onovo yana tuka kekensa

"Na karanci wani fanni na tattalin arziki, inda na samu shaidar kammala babbar Diploma da sakamako mai kyawun gaske sannan kuma na yi aiki har na tsawon shekaru hudu." In ji Onovo Ugochukwu.

Mista Onovo wanda matarsa ɗaya da ɗa ɗaya, ya ce yanzu haka a sana'ar tukin keke yake samun abin da yake daukar dawainiyar iyalin nasa.

Da alama dai wannan sana'a ta tukin keke da Onovo ke yi na da lagwada domin har kira ya yi ga sauran matasa irinsa.

Ya ce "ina kira ga matasa musamman masu babban karatu da ka da su rungume hannu suna jiran gwamnati ta ba su aiki domin ana cikin matsi a kasar nan saboda haka ku fito ku nemi sana'o'in da za ku dogara da kanku."

Hausawa dai na cewa babu maraya sai rago kuma Onovo Ugochukwu ya kasance babban misali ga kowa.

Image caption Onovo ya kwashe shekaru hudu yana aikin kamfani

Labarai masu alaka