Mutum 22 sun mutu a wani coci a Masar

Majami'ar St Mark's Cathedral a Masar

Asalin hoton, AFP

Akalla mutum 22 aka kashe bayan da wani abu ya fashe a kusa da wata majami'ar Kibdawa a Alkahira, babban birnin kasar Masar.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 08:00 agogon GMT wato (10:00 a kasar).

Akalla wasu karin mutum 10 sun samu raunuka kuma an garzaya da su asibiti.

Kafafen yada labarai sun ce babban jami'in da ke kula da tsaro na birnin Alkahira, Khalid Abdel Aal, ya isa domin ganin abin da ya faru.

Kawo yanzu dai ba a san abin da ya haddasa wannan fashewar ba.

Al'ummar Kiristoci sun kai kimanin kashi 10 cikin dari na jama'ar kasar.

Majami'ar ta St Mark's Cathedral ita ce cibiyar Kibdawa a kasar, kuma anan ne jagoransu Pope Tawadros II ya ke da zama.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda fashewar ta lalata wani bangare na saman ginin.