Wa zai zama gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na 2016?

Pierre-Emerick Aubameyang da Andre Ayew da Riyad Mahrez da Sadio Mane da kuma Yaya Toure

Pierre-Emerick Aubameyang ko Andre Ayew ko Riyad Mahrez ko Sadio Mane ko Yaya Toure. Daya daga cikin wadannan 'yan wasa ne zai lashe kyautar Gwarzon Kwallon Afirka na BBC na 2016 a ranar Litinin.

Masoya kwallon kafa a duniya baki daya ne suka zabi gwanin su a gasar ta 2016.

Za a rage sunayen 'yan kwallon daga biyar zuwa uku, ba bisa wata ka'ida ba, kuma kai-tsaye a tashar rediyo ta BBC mai yada shirye-shiryenta zuwa kasashen duniya, wato BBC World Service, da kuma a wannan shafin da karfe 3:40 daidai agogon GMT.

Za kuma a bayyana wanda ya lashe gasar kai-tsaye a tashar BBC Focus on Africa ta talabijin da rediyo da kuma wannan shafin da karfe 5:45 daidai agogon GMT.

Dan wasan gaba na Borussia Dortmund kuma dan kasar Gabon, Aubameyang, na cikin jerin sunayen 'yan takarar a shekara ta hudu ke nan a jere, a daya bangaren kuma dan wasan tsakiya na West Ham kuma dan kasar Ghana Andre Ayew--wanda ya lashe kyautar a 2011--yana cikin 'yan takarar a karo na hudu shi ma.

Dan wasan Leicester kuma dan kasar Algeria Mahrez, shi ne kadai dan wasan da bai taba shiga takarar ba a baya; shi kuwa dan wasan gaban Liverpool kuma dan kasar Senegal, Sadio Mane, ya shiga takarar a karo na farko a bara.

Kazalika dan wasan tsakiya a Manchester City kuma dan kasar Ivory Coast Yaya Toure ya jera shekara takwas yana shiga takarar, kuma sau biyu yana lashe kyautar.

Asalin hoton, CARMEN JASPERSEN

Bayanan hoto,

Aubameyang na cikin 'yan kwallon da suka fi taka rawa a gasar Bundesliga

Aubameyang mai shekaru 27, ya yi fice sosai a wasannin 2016, inda ya ci kwallo 30 a Dortmund.

Shi ne dan Afirka na farko da aka bayyana a matsayin fitaccen dan kwallon shekara a Bundesliga, kuma dan kasar Gabon na farko da ya zamo fitaccen dan kwallon shekara na CAF, lamarin da ya ba shi damar shiga jerin sunayen da aka tantace na kyautar Ballon d'Or.

A watan Agusta, West Ham ta kashe makudan kudin da ba ta taba kashe irin su ba wajen sayen Ayew; sun biya Swansea fam miliyan 20.5, lamarin da ya nuna muhimmancinsa a kakar wasannin 2016.

Asalin hoton, Michael Regan

Bayanan hoto,

West Ham na fatan Ayew zai taimaka mata sosai

Ficen da Ayew mai shekaru 26 ya yi a wasanni da kwallo 12 da ya ci a wasanni 35, ya sa aka masa lakabi da fitaccen sabon shiga a Swansea a karshen kakar wasanni a watan Mayu.

Wani dan wasan gasar Premier da ya samu nasara matuka a Leicester - kulob din da ba a yi wa zaton nasara ba ko kadan - shi ne Mahrez, ya kuma kai su ga lashe Kofin Gasar Premier.

Mahrez ya ci kwallo 17, kuma shi aka zaba a matsayin dan wasan da ya fi kowanne fice a bana - kuma shi ne karon farko da dan Afirka ke lashe wannan kyauta.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mahrez ne dan kwallon da ya fi kowanne taka leda a kakar bara

Ya kuma taka rawar gani a tawagar Algeria, har ya kai su ga samun gurbi a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta 2017.

Mane, mai shekaru 24, ya zamo dan kwallon Afirka da ya fi kowanne tsada a tarihi lokacin da Livepool ta biya fam miliyan 34 don sayen shi a bara.

Ya kuma taka rawar gani a Anfield, bayan ya zura kwallaye 15 wa kulob din.

Asalin hoton, PAUL ELLIS

Bayanan hoto,

Mane ya kai makura a rawar da yake takawa a Liverpool

Kafin komawarsa Liverpool, ya ci kwallo takwas a Southampton, ciki har da kwallo uku a cikin wasa daya; watau hat-trick- a karawarsu da Manchester City.

Toure ya sake lashe wata kyauta a 2016 - a karo na 17 ke nan a rayuwarsa ta kwallo - bayan ya daga Kofin Premier a Manchester City, inda ya buga fanaretin da ya fidda Liverpool a wasannin karshe.

Asalin hoton, OLI SCARFF

Bayanan hoto,

Toure ya taka rawar gani a shekara 15 da ta gabata

A bana ne dan wasan mai shekaru 33 ya bayyana yin ritaya daga buga wa kasarsa wasa.

Amma ya bayyana cewa har yanzu da sauran karfinsa, kuma ko a kwanan nan, Manchester City ta dawo da sa shi wasa.