'Dalilan da suka sa John Mahma faɗuwa zabe a Ghana'

zaben Ghana 2016

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A ranar Laraba aka gudanar da zabe a kasar Ghana

Da yammacin ranar Juma'a ne hukumar zaben Ghana ta bayyana jagoran 'yan adawa, Nana Akufo-Addo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi ranar Laraba.

Nana Akufo-Addo dai ya kayar da shugaba mai ci, John Mahma, bayan da ya samu kaso 53 na kuri'un da aka kada.

Rahotanni kuma sun ce John Mahma ya kira Nana Akufo-Addo ta waya, a inda ya taya shi murnar cin zaben.

Tuni dai mutane suka fara sanya ayar tambaya cewa wadanne dalilai ne suka sanya shugaban mai cin ya sha kasa.

Dalilan faduwar Mahma:

Wasu masu sharhi a Ghana na ganin wadannan dalilan ne suka sa John Mahma ya fadi zabe.

  • John Mahma ya hau mulki ba tare da manufa ba sakamakon mutuwar shugaban kasa John Attah Mills.
  • Wannan ne kuma ya janyo tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
  • Al'amarin da ya janyo tsadar rayuwa da hauhawar farashi kamar karin kudin ruwa da wuta da man fetir.
  • Cin hanci da rashawa da ya dabaibaye gwamnatin John Mahma
  • Ta'azzarar rashin aikinyi ga miliyoyin matasan kasar

A yanzu haka dai 'yan kasar ta Ghana na son sabon zababben shugaban ya mayar da hankali wajen sauya matsalolin da shugaba mai barin gado ya gadar wa kasar.