Nigeria: APC da PDP na fafatawa a zaben Rivers

Tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da kuma mai ci Nyesom Wike

Asalin hoton, Premium Times

Bayanan hoto,

Ba a ga-mu-ciji tsakanin Rotimi Amaechi da Nyesom Wike

Manyan jam'iyyu biyu da ke hamayya da juna a Najeriya na fafata wa a zabukan cike gurbi na 'yan majalisun jiha da tarayya a jihar Rivers.

Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar, wacce ta lashe zabukan a baya, kafin daga bisani kotu ta soke, na kokarin sake samun nasara.

Yayin da jam'iyyar APC mai mulkin kasar, amma 'yar adawa a jihar, ke ganin cewa za ta iya kai labari.

Jihar Rivers ta sha fama da rikicin siyasa wanda ke kara kaimi saboda takun-saka tsakanin tsohon gwamnan jihar Rotimi Amaechi da kuma mai ci Nyesom Wike.

Za a yi zabukan ne cikin zaman dar-dar domin kusan sau uku ke nan ake sa rana amma ana dagawa saboda dalilan rashin tsaro.

Sai dai a wannan karon hukumomi sun ce sun shirya inda aka tsaurara matakan tsaro a jihar baki daya.

Ko a ranar Juma'a sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kiran da a kwantar da hankali, yana mai cewa "ba batu ne na a mutu ko a yi rai ba."

'Yan majalisu 22 za a zaba a zabukan na ranar Asabar da suka hada da na majalisar dattawa da ta wakillai da kuma jiha.