Messi ya ci Osasuna kwallaye biyu

La Liga

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Lionel Messi ya ci kwallaye 22 kenan a kakar bana

Barcelona ta doke Osasuna da ci 3-0 a gasar La Liga wasan mako na 15 da suka kara a ranar Asabar.

Tun da farko Luis Suarez ya buga kwallo ta bugi turke a fafatawar da Barcelona ta mamaye ka-co-kan din wasan.

Luis Suarez din dai ne ya fara ci wa Barcelona kwallon, bayan da ya samu tamaula daga bugun da Jordi Alba ya yi masa.

Haka dai Jodi Alba ne ya bai wa Lionel Messi kwallo na biyu da ya ci Osasuna, kafin daga bayan dan wasan tawagar Argentina ya kara ta uku.

Barcelona tana matsayi na biyu a kan teburin La Liga da maki 31.