Bayern Munich ta koma kan teburin Bundesliga

Bundesliga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bayern Munich ta hada maki 33 daga wasanni 14 da ta yi

Bayern Munich ta koma mataki na daya a kan teburin Bundesliga na Jamus, bayan da ta casa Wolfsburg da ci 5-0 a fafatawar da suka yi a ranar Asabar.

Arjen Robben ne ya fara ci wa Munich kwallo a minti na 18 da fara tamaula, Robert Lewandowski ne ya ci ta biyu kafin a je hutu.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Lewandowski da Muller da Douglas Costa suka ci kwallaye.

Da wannan sakamakon Bayern Munich ta koma matsayi na daya a kan teburin Bundesliga da maki 33.

Wasu daga cikin sakamakon wasannin da aka yi:

  • Bayern Mun 5 VfL Wolfsburg 0
  • FC Ingolstadt 1 RB Leipzig 0
  • FC Köln 1 Bor Dortmd 1
  • Hamburger SV 1 FC Augsburg 0
  • SC Freiburg 1 Darmstadt 0