Ghana: 'Laifin 'yan majalisa ne ya shafi Mahama'

Nana Akufo-Addo ne ya lashe zaben da kaso 53

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba John Dramani Mahama ya sha kasa a zaben 2016

Wasu jagororin jam'iyya mai mulki a Ghana, NDC, wadda kuma yanzu tasha kasa a babban zaben kasar da aka yi ranar Laraba sun ce laifin 'yan majalisar jam'iyyar ya taimaka wajen kayar da shugaba Mahama.

Alhaji Audu Arif wanda mamba ne a kwamitin zartarwa na NDC, ya fadi cewa halayyar wasu 'yan majalisar ce ta janyo musu faduwa.

Ya ce "irin gudun jama'a da 'yan majalisar ke yi ce ta shafawa shugaba John Mahama bakin jini."

Audu Arif ya kara da cewa wasu ba su kara komawa mazabunsu ba tun daga ranar da aka zabe su har sai lokacin kamfe.