Nigeria: 'Yan 'shekara bakwai' ne suka kai hari Maiduguri

Asalin hoton, Getty Images
Mayakan Boko Haram na amfani da 'yan mata wajen kai harin kunar bakin wake
Rahotanni sun ce an yi amfani da wasu yara mata biyu 'yan shekara bakwai ko takwas wurin kai harin kunar bakin waken da ya kashe mutum guda tare da jikkata wasu 18, a birnin Maiduguri a ranar Lahadi.
'Yan sanda a babbn birnin na jihar Borno, a Kudu maso Gabashin Najeriya, sun ce an kai harin ne lokacin da kasuwar ke makare da masu sayayya.
Shaidu sun ce matan sun tayar da ababen fashewar ne 'yan mintina tsakanin juna, kuma dukkansu sun mutu.
Wani dan kato-da-gora ya ce 'yan matan da suka kai sun zo ne a cikin babur mai kafa uku wato Keke Napep.
Ya kuma yi kokarin tsaida daya daga cikinsu, amma sai taki tsayawa tare da nufar taron wasu mutane da ke saida kaji, ba tare da bata lokaci ba ta tada bam din da ke jikinta.
A lokacin da mutane suka taru dan kaiwa wadanda suka jikkata dauki, ita ma dayar yarinyar sai ta tashi bam din da ke jikin ta.
Lamarin da ya sanya kasuwar ta yamutse aka fara gudun ceton rai.
Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari.
Sai dai a baya Boko Haram ta sha kai hare-hare a kasuwannin da ke cikin birnin da ma kauyuka har da jihohin Adamawa da Yobe masu makoftaka da jihar Borno.
Harwayau kungiyar na yawan amfani da 'yara mata kanana da 'yan mata har ma da tsofaffi wajen kai harin kunar bakin wake a jihohin arewa maso gabashin kasar.