Bangladesh ta rufe wa Musulman Rohingya kofa

Myanmar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daya daga cikin masu gadin kan iyakoki a Bangladesh

Masu gadin kan iyaka a Bangladesh sun ce sun kora akalla karin jiragen ruwa goma sha uku dauke da Musulman kabilar Rohingya daga Myanmar.

An mayar da 'yan gudun hijiran ne zuwa yankin dake cikin kasar Myanmar a cikin teku, bayan jami'ai sun tare su.

Bangladesh ta tsuke iyakokinta sosai, don hana kwararar 'yan kabilar Rohingya cikin kasar.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane dubu goma ne suka fice daga Myanmar a 'yan makonnin nan.

Mutanen sun gudu ne saboda bude wuta da sojojin Myanmar ke ci gaba da yi da sunan yaki da 'yan bindiga, wanda rahotanni suka ce ya shafi fararen hula da yawa.