Dan jarida mai yajin cin abinci ya mutu a Aljeriya

Algeria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika

Dan jaridan nan, dan Burtaniya amma dan asalin Aljeriya wanda ya shiga yajin cin abinci saboda daure shi da aka yi akan ya yi wa shugaban Aljeriya laifi, ya mutu a asibiti.

Lauyan Mohamed Tamalt ya ce tun a watan Agusta, dan jaridan yake cikin hali irin na suma a asibiti a Bab el-Oued.

A watan Yuni ne aka tsare shi lokacin da ya kai wata ziyara Aljeriya daga London, inda yake tafiyar da wani shafi na intanet.

An yake mushi daurin shekaru biyu a gidan yari, tare da cin shi tarar dala dubu biyu, bisa alakanta shi da wani bidiyo da aka yada a shafin Facebook.

A baya dai, kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi kiran da a sake shi.