Gambia: Jammeh zai garzaya kotun koli

Tun da farko Mr Jammeh ya amince da shan kaye har ya taya Mr Barrow murnar lashe zaben.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Tun da farko Mr Jammeh ya amince da shan kaye har ya taya Mr Barrow murnar lashe zaben.

Jam'iyyar da shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya tsaya takara ta ce shugaban kasar zai garzaya kotun koli don kalubalantar sakamakon zaben.

Hukumar zaben kasar dai ta sanar da dan takaran jam'iyyar adawa Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben.

Tun da farko Mr Jammeh ya amince da shan kaye har ya taya Mr Barrow murnar lashe zaben.

Sai dai a wani jawabi na ba zata da yayi ranar juma'a, shugaban ya ce sam ba zai amince da sakamakon zaben ba.

Matakin da Mr Jammeh ya dauka dai ya janyo kakkausar suka daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar tarayyar Afrika.

Wata sanarwa da Shugabar kungiyar tarayyar Afrika Dlamini-Zuma ta fitar, ta yi kira ga Shugaba Jammeh da ya tabbatar ya bayar da hadin kai wurin mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin lumana.

Ita ma Amurka ta nuna takaicinta kan yadda shugaban mai barin gado ya sauya matsaya kan sakamakon zaben.

A 1994 dai Yahya Jameh ya hau mulkin kasar, bayan juyin mulkin da ya jagoranta a kasar.

Mista Barrow ya zargi shugaban mai ci da kokarin lalata tsarin demokuradiyya ta hanyar yin kin amincewa da sakamakon zaben.

Sai dai jami'ansa sun ce shugaba mai jiran gadon yana nan cikin koshin lafiya.

Hukumar zaben kasar ta sake duba sakamakon zaben a ranar 5 ga watan Disamba bayan da aka gano cewa an yi kuskure a wata mazaba, abin da ya kara wa Mista Barrow yawan kuri'u.

Kuskuren ya haifar da kara kuri'u ga wasu 'yan takarar, sai dai bai sauya yadda sakamakon ya kasance ba, a cewar hukumar.

Sai dai ya rage adadin tazarar da Mista Barrow ya bayar daga kashi 9 cikin dari zuwa kashi 4.