Zan farfado da tattalin arzikin Ghana - Akufo-Addo

Nana Addo ya samu kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Nana Addo ya samu kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada

Zababben Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya ce farfado da tattalin arzikin kasar shi ne babban abin da zai sa a gaba da zarar ya kama aiki.

A hirar sa ta farko da BBC tun bayan da aka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben, Mista Akufo-Addo ya kawo karshen rashin ayyukan yi tsakanin matasa.

"Tattalin arzikin Ghana ya shiga wani yanayi maras kyau a shekara biyar da ta wuce, ga rashin ayyukan yi, ga dimbin bashi, wannan shi ne halin da muke cikin," in ji shi.

Tun a lokacin yakin neman zabe, Mista Akufo-Addo ya yi alkawarin kafa masana'anta a dukkan mazabun kasar.

Da yake tsokaci kan batun cin hanci da rashawa, ya zayyana irin matakan da zai dauka don magance matsalar inda ya jaddada aniyarsa ta tsame siyasa daga duk wani bincike na aikata laifuffuka.

Ya ce zai kafa ofishin mai gabatar da kara na musamman domin yaki da matsalar.

Shi dai Mr Nana Addo ya lashe zaben ne da kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada inda abokin takararsa shugaban mai ci John Dramani Mahama ya samu kashi 44.

Wannan ne dai karon farko da shugaba mai ci ke shan kaye a zabe a tarihin kasar Ghana.

A watan da ya gabat ne zai karbi ragamar mulkin kasar.