Tattalin arzikin Kuwait ya shiga mawuyacin hali

Sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmed al-Jaber al-Sabah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmed al-Jaber al-Sabah

Sarkin Kuwait ya ce babu makawa sai an rage kudaden da gwamnati ke kashewa sakamakon faduwar da farashin danyen mai yayi a duniya.

Da yake jawabin bude zauren sabbin 'yan Majalisun dokokin kasar, Sheikh Sabah al-Ahmad ya ce akwai bukatar a yi nazari sosai na yawan kudaden da za'a rage domin ciki wagegen gibi a kasafin kudin kasar.

Ya kara da cewa ya kamata a yi la'akari da masu karamin karfi a matakin tsuke bakin aljihu da gwamnati ta bullo da shi.

Akasarin 'yan Majalisun dokokin da aka zaba a watan Nuwamba dai sun sha alwashin kin amincewa da zabtaren kudin da gwamnati ke kashewa wajen samar da ababen more rayuwa.

Sai dai Firai ministan kasar Sheikh Jaber al-Mubarak ya shaidawa 'yan Majalisun cewa za a fadada tattalin arzikin kasar ta yadda za'a daina dogaro da man fetur kadai.

Kudaden da Kuwait ke samu wajen sayar da danyen mai dai ya yi matukar raguwa da kusan kashi 60 cikin shekaru biyu.