Bam ya hallaka mutum daya a Borno

Har yanzu babu wadanda suka dauki alhakin kai harin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Har yanzu babu wadanda suka dauki alhakin kai harin

Jami'ai sun ce akalla mutum daya ne ya rasa ransa yayin da mutum 17 suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin wake da wasu mata biyu suka kai a wata kasuwa dake birnin Maiduguri na jihar Borno.

Wani jami'i na kungiyar 'yan sintiri na farar hula a garin Maiduguri ya ce maharan mata biyu wadanda suma suka mutu shekarun su basu wuce bakwai zuwa takwas ba.

Babu wata kungiya data dauki alhakin kai wannan harin na ranar Lahadi sai dai kungiyar Boko Haram ta sha amfani da mata da kananan yara wajen kai hare haren kunar bakin wake da kan janyo asarar rayuka.

A kwanakin baya ne dai Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya tabbatarwa kasashen duniya cewa ana dab da kawo karshen Boko Haram.

Shugaba Buhari ya ce jama'a musamman mazauna shiyyar arewa maso gabashin kasar sun tabbatar cewa babu wata karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 774 na kasar dake hannun 'yan Boko Haram.