Venezuela za ta sauya takardar kudinta zuwa sulalla

Asalin hoton, Getty Images
Cikin kwanaki 3 gwamnati ta ce za ta sauya takardar kudin zuwa sulalla
Gwamnatin Venezuela ta sanar d cewa zata sauya babbar takardar kudin kasar zuwa sulalla cikin kwanaki uku.
Kasar dai na fatan matakin zai hana fasakwauri tare da rage karancin abinci da sauran kayayyaki da ake fuskanta.
Shugaba Nicolas Maduro ya ce gungun masu fasakwauri dake kaiwa da komawa akan kan iyakokin kasar ba zasu samu isasshen lokacin da zasu kwashe kudaden su domin canzawa ba.
Darajar takaardar kudin kasar wato bolivar 100 ya yi matukar faruwa a yan shekarun nan inda yanzu dajarar ta bata kai Centi 2 na kudin Amurka.
A kasar Indiya ma an dauki irin wannan mataki a watan daya gabata na daina amfani da babbar takardar kudin kasar, lamarin daya haddasa rudani.