Zakarun Turai: Arsenal za ta kara da Bayern Munich

Bayern ta sha fitar da Arsenal a wannan zagayen

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal za ta kara da Bayern Munich a zagayen 'yan 16 na gasar cin kofin zakarun Turai.

Ita kuwa Leicester City za ta hadu ne da Sevilla, sai kuma Manchester City da za ta kece raini da Monaco.

Sau hudu Gunners na haduwa da zakarun na Jamus a shekara biyar da ta gabata, amma kuma duka Bayern ce ke samun nasara.

Daya daga cikin manyan wasannin su ne karawar da za a yi tsakanin Barcelona da Paris St-Germain.

Barca ta doke PSG a kan hanyarta ta lashe gasar a kakar 2014-15.

Masu rike da kanbun kuma jagororin La Liga Real Madrid za su kara da Napoli na kasar Italiya, wadanda suke matsayi na hudu a gasar Serie A.

Ga wasannin dalla-dalla:

Manchester City v Monaco

Real Madrid v Napoli

Benfica v Borussia Dortmund

Bayern Munich v Arsenal

FC Porto v Juventus

Bayer Leverkusen v Atletico Madrid

Paris St-Germain v Barcelona

Sevilla v Leicester