Gwarzon kwallon Afirka: Mutum biyu ne suka rage a takara!

Riyad Mahrez da Sadio Mane
Bayanan hoto,

Wa zai lashe kyautar cikin Riyad Mahrez dan kasar Algeria ko dan kasar Senegal Sadio Mane?

Masoya kwallo a fadin duniya ne suka zabi wanda suke so ya lashe kyautar a 2016.

Tuni aka rage sunayen 'yan takarar wadanda su biyar ne, inda aka cire Pierre-Emerick Aubameyang da Andre Ayew da Yaya Toure ranar Litinin.

Za a bayyana wanda ya lashe gasar kai-tsaye a tashar BBC Focus on Afirka ta talabijin da rediyo da kuma shafin mu na intanet daga karfe 5:45 agogon GMT.

Wannan shi ne karo na farko da dan wasan gaban Leicester, kuma dan Algeria, Mahrez ya samu shiga takarar.

Dan wasan gaban ya haskaka sosai bayan ficen da ya yi a Gasar Premier ta Ingila--inda kungiyarsa ta yi nasarar ba-zata ta daga kofin a karo na farko.

Ya ci kwallo 17, kuma an zabe shi a matsayin dan wasan da ya fi kowanne fice a bana - dan Afirka na farko da ya taba lashe kyautar.

Ya kuma taka rawar gani a tawagar Algeria, har ya kai su ga samun gurbi a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta 2017.

Mane, mai shekaru 24 ya zamo dan kwallon Afirka da ya fi kowanne tsada a tarihi lokacin da Livepool ta biya fam miliyan 34 don sayen shi a bazarar da ta gabata.

Ya kuma taka rawar gani a Anfield, bayan ya zura kwallaye 15 wa kulob din.

Kafin komawarsa Liverpool, ya zura kwallaye takwas a Southampton, ciki har da kwallaye uku a wasa daya; watau hat-trick- a karawar su da Manchester City.

Duk dai wanda ya lashe gasar a cikin su, zai shiga sahun manyan 'yan kwallon da suka lashe kyautar a baya, irin su Mohamed Aboutrika, da Jay-Jay Okocha, da kuma Didier Drogba.