Ronaldo ya lashe kyautar Ballon D'or

Ronaldo ya lashe kyautar Ballon D'or

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ronaldo ya lashe kyautar Ballon D'or

An bayyana sunan Cristiano Ronaldo a matsayin wanda ya lashe kyautar Ballon D'or, ta dan kwallon kafar da ya fi nuna bajinta a duniya a bana.

Wannan ne karo na hudu da dan wasan na kulob din Real Madrid ke lashe kyautar.

Ronaldo, mai shekaru 31, wanda ya ci kofin zakarun kulob na Turai, da kuma kofin nahiyar Turai da kasarsa Portugal, a 'yan watanin da suka wuce, ya karbe kambin zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya ne daga babban abokin hamayarsa na Barcelona, Lionel Messi.