Nigeria: Kashi 29 na cibiyoyin lafiya ba su da ruwa

Jarkokin ruwa a cibiyar kula da lafiya ta Garki Village

Asalin hoton, WaterAid/ Simi Vijay

Bayanan hoto,

An jera jarkokin ruwan sayarwa a Cibiyar Kula da Lafiya Matakin Farko dake Garki Village, inda ake sayen ruwa saboda rashin ruwa a cibiyar

Wani rahoto da aka fitar albarkacin Ranar Samar da Lafiya ga Kowa ta Duniya ya bayyana cewa a duk cibiyoyin kiwon lafiya na Najeriya uku, kusan guda biyu na fama da rashin ruwa.

Rahoton, wanda kungiyar WaterAid Nigeria mai fafutukar ganin an samar da tsaftataccen ruwan sha da ingantaccen magewayi ta fitar, yana dauke da hotunan wasu cibiyoyin kiwon lafiya a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ko dai ake sayen ruwa a jarka, ko kuma babu magewayi mai kyau.

Rahoton ya ambato Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, na cewa kashi 42 cikin 100 na cibiyoyin kula da lafiya a nahiyar Afirka kudu da Sahara ba su da ruwa mai tsafta, sannan ya kara da cewa, "A Najeriya kashi 29 cikin 100 na manya da kananan asibitoci ba su da tsaftataccen ruwa, kuma wani adadi kwatankwacin haka na asibitocin ba su da magewayi mai kyau, yayin da kashi 16 cikin 100 ba su da wurin wanke hannu da sabulu".

Shugaban kungiyar ta WaterAid a Najeriya, Dr Michael Ojo, ya bayyana cewa, "Sau da dama, cibiyoyin kula da lafiya a kasashe masu karamin karfi na fama da karanci ko ma rashin ruwa, da rashin tsafta, da kuma rashin hanyoyin kawar da shara masu tsafta. Hakan na hana ma'aikatan lafiya kula da marasa lafiya yadda ya kamata, ya kan kuma jefa likitoci, da ungozomomi, da ma'aikatan jinya, da masu goge-goge/share-share, da ma marasa lafiya cikin mummunan hadarin kamuwa da cututtuka".

Kungiyar ta WaterAid Nigeria ta ce wani bincike da ta gudanar a wadansu jihohi shida ya nuna cewa kashi 21.1 cikin 100 na cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko ba su da magewaye akalla guda daya, sannan ba su cika sharadin Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ba na samar da magewayi daban-daban ga mata da maza da kuma bambanta magewayin ma'aikatan lafiya da marasa lafiya.

Asalin hoton, WaterAid/ Simi Vijay

Bayanan hoto,

Yanayi mara kyau a daya daga cikin wuraren da marasa lafiya ke gewayawa a karamin asibitin garin Gwagwalada, Abuja, a watan Satumba 2016

Bugu da kari, inji rahoton, a jihohin shida, kashi 20.2 cikin 100 ne kacal na cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko ke da wurin wanke hannu a magewayinsu; sannan kuma kashi 54.9 cikin 100 na cibiyoyin da aka tantance ne ke da wuraren wanke hannu a dakin karbar haihuwa.

Kungiyar ta kuma bukaci masana harkar kula da lafiya da su sa baki wajen kira ga gwamnatoci da su hanzarta samar da tsaftataccen ruwa da magewayi a dukkan cibiyoyin kula da lafiya yayin da ake bikin Ranar Samar da Lafiya ga Kowa ta Duniya.

An dai ayyana ranar 12 ga watan Disamban ko wacce shekara a matsayin Ranar Samar da Lafiya ga Kowa ta Duniya ne da nufin jaddada bukatar samar da lafiya ga kowa ba tare da wata wahala ba.

Yunkurin jin ta-bakin hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, wadda rahoton ke dauke da hotunan cibiyoyin kula da lafiyarta, bai yi nasara ba, saboda wayar babban jami'inta na yada labarai, Muhammad Hazat Sule, ba ta tafiya, kuma har zuwa lokacin kammala wannan rahoton bai amsa sakonnin text da na email da muka aike mishi ba.