Ronaldo ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2016

Ballon d'Or 2016

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karo na hudu Ronaldo yana lashe kyautar Ballon d'Or

Dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya lashe kyautar dan kwallon kafa na duniya da ya fi yin fice a bana, wato kyautar Ballon d'Or.

Ronaldo mai shekara 31, ya taimakawa Real Madrid lashe kofin zakaraun Turai a bara, ya kuma ci kwallaye uku da suka bai wa Portugal damar cin kofin nahiyar Turai a 2016.

Dan wasan na Real Madrid ya ci kyautar Ballon d'Or karo na hudu kenan, bayan 2008 da 2013 da kuma 2014.

A tarihin lashe kyautar Lionel Messi ne ke kan gaba, wanda ya karbi guda biyar a shekarar 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da kuma 2015.