"Mun kusa murkushe Boko Haram"

Hukumomin tsaron Nigeria sun bukaci al'umma da su bada rahoton duk wani mutum da basu amince da shi ba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hukumomin tsaron Nigeria sun bukaci al'umma da su bada rahoton duk wani mutum da basu amince da shi ba

Hedikwatar tsaron Nigeria ta ce nan bada jimawa ba zata kawo karshen mayakan Boko Haram da suka addabi al'ummar shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun hedikwatar tsaron Birgediya Janar Rabe Abubakar shine ya bayyana haka a wata hira da BBC.

Ya ce a halin yanzu jami'an sojin kasar sun karya lagon mayakan kungiyar kuma zasu ci gaba da bin duk inda suka boye su murkushe su.

Sai dai duk da kokarin da hukumomin tsaro ke cewa suna yi na fatattakar mayakan Boko Haram, har yanzu 'yan kungiyar na iya kai hare-hare da kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Ko a farkon watan Nuwamban da ya gabata an kai wasu hare-haren kunar bakin wake a wata kasuwa mai cunkoson jama'a a garin Madagali dake jihar Adamawa, da kuma a birnin Maiduguri inda aka samu asarar rayukan mutane da dama.

Sai dai hukumomin tsaron Nigeria sun bukaci al'umma da su ci gaba da bada rahoton duk wani mutum da basu amince da shi ba, inda suka nanata cewa babu makawa karshen Boko Haram ya zo kusa.

Shima Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari a kwanakin baya ya tabbatarwa kasashen duniya cewa ana dab da kawo karshen Boko Haram.