An rantsar Guterres a matsayin sakataren MDD

Antonio Guterres zai fara aiki ne daga watan Janairun shekarar 2017 bayan cikar wa'adin Ban Ki-Moon
Bayanan hoto,

Antonio Guterres zai fara aiki ne daga watan Janairun shekarar 2017 bayan cikar wa'adin Ban Ki-Moon

An rantsar da tsohon Firai ministan kasar Portugal Antonio Guterres, a matsayin sabon sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai jiran gado.

Zai fara aiki ne daga watan Janairun shekarar 2017 na tsawon shekaru biyar bayan cikar wa'adin Mr Ban Ki-Moon.

Da yake jawabi ga taron koli na Majalisar, Mr Guterres ya ce wajibi ne a yi gyare-gyare a Majalisar domin aiki kamar yadda ake bukata.

Ya kara da cewa akwai bukatar Majalisar ta kara sauraren koke koke tare da daukar matakai don tabbatar da hadin kai.

Ya ce an kafa Majalisar ne sakamakon yake-yake a don haka wajibi ne mu nemi zaman lafiya.