Kananan yara na mutuwa a Yemen

Akalla yaro daya ne ke mutuwa cikin kowane minti goma sakamakon kamuwa da cututtuka

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Akalla yaro daya ne ke mutuwa cikin kowane minti goma sakamakon kamuwa da cututtuka

Ma'aikatan agaji sun ce kananan yara fiye da miliyan biyu ne a Yemen ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ce akalla yaro daya ne ke mutuwa cikin kowane minti goma sakamakon kamuwa da cututtukan da ake iya magance su.

Yemen ta kasance cikin kasashen da suka fi talauci a duniya tun ma kafin yakin daya barke a shekarar data gabata.

Har yanzu dai ana ta gumurzu tsakanin dakarun gwamnati da mayakan 'yan tawayen Houthi.

Acewar UNICEF ba'a iya samun damar kai kayayyakin abinci zuwa yankuna da dama da ake matukar bukata, kuma halin da ake ciki ya yi matukar muni sosai.