Sojojin Syria na gab da karbo birnin Aleppo

Iyalai cikin mawuyacin hali
Bayanan hoto,

Fararen hula, mata da kananan yara su ne suka fi shan wahala a yakin da ake yi a Syria

Alamu sun fara nuna ta yiwu ana gab da kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 4 ana yi na neman kwace iko da birnin Aleppo na kasar Syria.

Gidan talabijin din kasar ya nuna yadda fararen hula a wasu yankuna birnin, su na ta murna bayan da sojoji suka kutsa cikin yankunan da 'yan tawaye suka mamaye.

Jagoran dakarun Syria Laftanal janar Zaid al-Saleh, ya shaida wa manema labarai a gundumar Sheikh Sa'eed cewa ya kamata a kawo karshen yakin da ake yi a yammacin birnin Aleppo, saboda 'yan tawayen ba su da sauran karfin iko a yankin, ko dai su mika wuya ga sojojin gwamnati ko kuma a karasa murkushe su.

A yankunan da gwamnati ke iko da su kuwa, sojoji ne ke ta shagulgulan nasarar da suka samu, su na ta harba harsashai sararin samaniya, ya yin da motoci ke ta yin kwabo.

Shugaban 'yan tawayen kungiyar Fastaqim, Zakaria Malahifji, yace halin da suke ciki ya yi muni sosai, ya yin da jami'in kungiyar Jabna Shamiyya ke bada rahoton irin mawuyacin halin da suke ciki.

A man pushes a cart carrying an elderly woman and belongings as they flee deeper into the remaining rebel-held areas of Aleppo, Syria December 12, 2016

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jama'a na kokarin barnin na Aleppo

Kungiyar white helmets kuwa mai taimakawa fararen hula ta ce ta shirya tsaf don samawa fiye da fararen hula dubu daya hanyar da za su koma yankunan da gwamnati ke iko da shi.

Yayin da wasu daga cikin fararen hula suka yanke kaunar ci gaba da rayuwa, su na ta wallafa wasiyya da sakon bankwana ga 'yan uwansu a shafukan sada zumunta da muhawara, saboda ba sa tunanin za su kara rayuwa nan gaba.

Free Syrian Army fighters gather in a rebel-held area of Aleppo, Syria December 12, 2016.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wadannan mayakan na 'yan tawaye na cigaba da zama a yankunan da suke iko da su