Shugabannin Afirka na kokarin sasanta rikicin siyasar Gambia

Yahya Jameh
Bayanan hoto,

Sai bayan ya amince da shankaye a zaben, sannan shugaba Jameh ya tubure bai aminta da sakamakon zaben ba

Kungiyar lauyoyi ta kasar Gambia ta yi alla-wadai da kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar da shugaba mai ci Yahya Jammeh yayi inda ta bayyana hakan a matsayin cin amanar kasa.

Kungiyar ta kuma bukaci mambobinta da su kauracewa zama a kotuna har sai shugaba Mr Jammeh ya mika mulki.

A ranar Talata ne kuma tawagar wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka za su isa Gambia domin sasanta rikicin siyasar kasar, cikin su har da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu takwarorinsa na Yammacin Afirka za su gana da Shugaba Jameh domin sasanta rikicin siyasar da ya barke a kasar.

An shiga rudani ne bayan da Shugaba Yahya Jammeh ya ki amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a farkon wannan watan.

Tawagar da ake sa ran za ta kunshi Shugabannin kasashen Liberia da Ghana, za ta kuma tattauna da shugaba mai jiran gado Adama Barrow.

Tuni dai Mista Barrow ya yi kira ga kasashen duniya da su tilastawa Mista Jammeh ya sauka daga mulki ba tare da bata lokaci ba.

A bangare guda kuma Kwamitin tsaro na MDD ya tattauna rikicin kasar na Zambia.

Juan Manuel Gonzalez de Linares Palou, shi ne mataimakin jakadan Spaniya a MDD wanda ya karanta jawabi a madadin sauran 'yan kwamitin.

Ya ce mambobin kwamitin sun sake kira ga shugaba Jammeh mai barin gado daya mutunta zabin al'ummar Gambia ya mika mulki ba tare da wasu sharudda ko bata lokaci ba ga zababben shugaban kasar Mr. Adam Barrow.