Gwamnan Jakarta ya fashe da kuka a kotu bisa zargin yin sabo

Gwamnan birnin Jakarta na Indonesia, Basuki Tjahaja Purnama

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Ana watsa shari'ar kai tsaye a gidan talabijin na kasar

An nuna jimami a ranar farko ta shari'ar da ake yi wa gwamnan birnin Jakarta na Indonesia kan zargin aikata sabo.

Basuki Tjahaja Purnama, wanda aka fi sani da Ahok, ya fashe da kuka a lokacin da yake musanta zargin yin batanci ga addinin Musulunci.

Mr Purnama, wanda Kirista ne dan kabilar Sin, shi ne mutumin da ba Musulmi ba na farko da ya jagoranci birnin a cikin shekara 50.

Ana yi wa shari'ar kallon wani zakaran gwajin dafi a kasar wacce ita ce ta fi yawan Musulmai a duniya.

Masu gabatar da kara sun ce Mista Purnama ya soki Musulmi ta hanyar yin amfani da ayar Alkur'ani ba bisa ka'ida ba, wacce ta ce bai kamata wanda ba Musulmi ba ya jagoranci al'ummar Musulmi.

Sun kara da cewa ya yi hakan ne domin samun kuri'u a lokacin yakin neman zabe a watan Fabrairu.

Ya nace cewa ya yi jawabin ne saboda 'yan siyasa wadanda suke "amfani" da ayar domin hanawa a zabe shi, amma ba wai ayar yake suka ba.

Idan har aka same shi da laifi, zai fuskanci daurin shekara biyar.

Bayan an saurari shari'ar na wani dan lokaci, alkalin kotun ya dage zaman zuwa 20 ga watan Disamba.