An gurfanar da wani Basaraken Uganda a kotu

Wesley Mumbere

An tuhumi wani Basaraken kasar Uganda da laifin ta'addanci da yunkurin kisa da kuma fashi a lokacin da ya gurfana a wata kotu cike da magoya bayansa.

A watan da ya gabata ne aka kama Wesley Mumbere bayan wani sumame da jami'an tsaro suka kai fadarsa, inda mutum 80 suka mutu.

Babu tabbas ko tuhumar ta'addancin na da alaka da tashin hankalin na baya-bayan nan ko kuma shari'ar da ya ke fuskanta bisa zargin kashe wani jami'in dan sanda a watan Maris.

Lauyan Basaraken ya fada wa BBC cewa an kuma gurfanar da wasu mazaje su 12 a kotu, da suka hada da dogaransa da kuma wani boka.

Kuma kawo yanzu ba a nemi su da amsa laifi ko kuma akasin haka ba.

'Yan sanda sun tsare daruruwan mutane a lokacin da suka kai sumamen na watan da ya gabata.

Kafin ya zama sarki, Mr Mumbere ya shafe shekaru yana zama a Amurka, inda ya yi aiki a wani gidan kula da yara a Pennsylvania.