Ba mu cimma yarjejeniya da Jammeh ba-ECOWAS

Shugaban Gambia Yahya Jameh da Muhammadu Buhari na Najeriya da John Mahama na Ghana

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da Yahya Jammeh ya gana da wasu shugabannin kasashen waje tun bayan zaben

Shugabar kasar Liberian Ellen Johnson Sirleaf, wacce ta jagoranci wata tawagar shugabannin kasashen yammacin Afrika don sasanta rikicin siyasar kasar Gambia ta ce babu wata yarjejejeniya da suka cimma don kawo karshen dambarwar.

Tun da farko dai Sojoji a Gambia sun mamaye hedikwatar hukumar zabe yayin da Jam'iyyar Mr Jammeh ta shigar da kara a kotun kolin kasar inda ta bukaci a soke zaben.

Sai dai a halin yanzu kotun bata da isassun Alkalai, saboda haka ba a san takamammen lokacin da za a saurari karar ba.

A baya dai Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Marcel de Souza, ya yi barazanar cewa za su yi amfani da karfi idan Mista Jammeh ya ki mutunta kundin tsarin mulkin kasar.

Zababben shugaban kasar Adama Barrow, wanda ya lashe zaben na 1 ga watan Disamba, ya nemi taimakon kasashen duniya.

A watan gobe ne ya kamata a rantsar da shi a kan karagar mulki.

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya ce za su nemi Mista Jammeh ya mutunta tsarin mulki

Shugaba Buhari ya ce Shugaba Yahya Jammeh ya yi musu kyakkyawar tarba a ganawar da suka yi da shi a asirce na tsawon sa'a guda.

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto,

Kusan Yahya Jammeh ne kawai yake fara'a a wannan hoton