Batun Super Falcons: An gayyaci ma'aikatar wasanni da NFF

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Najeriya Super Falcons

Asalin hoton, Ayodeji

Bayanan hoto,

Shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa ne Malam Abba Kyari ya tarbi 'yan matan

Wasu Rahotanni a Najeriya sun ce an gayyaci jami'an ma'aikatar wasanni da hukumar kwallon kafa ta kasar zuwa fadar shugaban kasar kan batun yan wasan kwallon kafa mata na Super Falcons.

A ranar Larabar nan ne 'yan wasan suka yi zanga-zanga zuwa Majalisar Dokoki da fadar Shugaban kasar a kan kin biyansu kudaden da ya kamata a ba su, bayan sun ci kofin Afirka karo na 8 a Kamaru, ranar 3 ga watan Disamba.

A lokacin zanga-zangar tawagar ta gabatar da korafi ga shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasar Malam Abba Kyari, wanda ya ce gwamnati na sane da halin da suke ciki.

Ya kuma yi musu alkawarin cewa za a shawo kan lamarin cikin kwana biyu, kamar yadda daya daga cikin wadanda suka shirya macin ta shaida wa BBC.

Ta kara da cewa a yanzu 'yan wasan sun koma otal din Agura inda suke zaman dirshan, domin jiran alkawarin da gwamnati ta yi musu.

Jama'a na ta yada hotunan 'yan matan dauke da kwalaye a shafukan sada zumunta, inda mafi yawan mutane ke goyon bayansu.

Ba wannan ne karo na farko da 'yan wasan Najeriya ke kokowa kan rashin biyansu hakkinsu a kan ka'ida ba.

Asalin hoton, Ayodeji

Bayanan hoto,

'Yan matan na zaman dirshan a otel din Agura da ke Abuja

Asalin hoton, Ayodeji

Bayanan hoto,

Malam Abba Kyari ya bai wa 'yan wasan hakuri tare da yin alkawarin za a biya musu bukatunsu