Buhari: Ba za a kashe kudin gwamnati a auren Zahra ba

Zahra Buhari da saurayinta Ahmed Mohammed Indimi

Asalin hoton, Aisha Buhari

Bayanan hoto,

Mahaifiyar Zahra, Aisha Buhari, ta wallafa hotonta da wanda zai aureta a shafinta na Twitter

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce ba za a kashe ko kwabo daga kudin gwamnati ba a bikin 'yarsa Zahra, wanda za a yi a karshen makon nan.

Bikin Zahra da Ahmed Mohammed Indimi - da ga hamshakin dan kasuwar nan dan asalin jihar Borno, Mohammed Indimi, ya ja hankali, inda ake rade-radin cewa an shirya kashe makudan kudade domin cashe wa.

Sai dai wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce wannan biki ya shafi shugaban da iyalansa ne kurum, don haka babu ruwan gwamnati a ciki.

"Ba a yi amfani da kudin gwamnati wurin buga katin gayyata ba ko kuma sayen kayan bikin da za a raba ba," a cewar sanarwar, wacce mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya fitar.

Ya kara da cewa, Shugaba Buhari ya nemi a bashi lissafin kudaden da za a kashe a wurin bikin, inda daga bisani ya jadda cewa ba ruwan gwamnati a duk abin da za a yi.

"Wannan ya nuna irin nagartar Shugaba Buhari," a cewar Malam Garba Shehu.

A ranar Alhamis ne aka fara bikin, inda za a daura aure a ranar Juma'a, sannan a yi walima ta maza da kuma fati na mata, kafin daga bisani a kai amarya dakinta a karshe mako.

"Duk irin yadda dangi ke son su yi murnar auran 'yarsu, ba za a wuce gona-da-iri ba, in ji Garba Shehu.

Ya kuma bayyana cewa dangi da masu taimakawa shugaban ne, suka hada kudaden da za a yi bikin da su.

Babu tabbas ko wadannan kalamai za su gamsar da 'yan kasar, wadanda talauci ya yiwa katutu, musamman idan aka wuce gona-da-iri a wurin bikin.