Luwadi: 'Yan wasa 3 a Ingila na shirin sanarwa su 'yan luwadi ne

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan wasan Aston Villa da West Ham Thomas Hitzlsperger bayan ya gama wasa a Ingila ya bayyana cewa shi dan luwadi ne
Wasu 'yan wasan kwallon kafa uku na gana wa da hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, kan yadda za su fito fili su gaya wa duniya cewa su masu neman maza ne.
Wani dan majalisar dokokin Birtaniya John Nicolson ne ya bayyana haka, a yayin zaman jin bahasi kan zargin lalata da matasan 'yan wasa da wasu tsoffin koci-koci suka yi.
A watan Oktoba shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, Greg Clarke ya gaya wa 'yan majalisar dokokin Birtaniya cewa 'yan wasan gasar Premie za su fuskanci matukar cin zarafi idan suka fito fili suka bayyana cewa su 'yan luwadi ne.
A lokacin da take magana da dan majalisa Nicolson, ministar wasanni ta Birtaniyar Tracey Crouch ta ce, " babu wani lokaci da ya wuce yanzu da ya fi dacewa 'yan wasan masu neman jinsi daya su fito su fada.''
Ministar ta ce: ''Kalaman da shugabn hukumar kwllon ta Ingila, Clarke ya yi cewa duk dan wasan da ya fito fili ya bayyana kansa zai sha tsangwama, abu ne da bai dace ba, kuma wani bako.
Ta kara da cewa: "Duk wanda ya yanke shawara ya fito ya bayyana kansa, to ya dauka cewa hukuma tana goyon bayansa.
kuma duk wani wulakanci ko cin zarafi da aka yi masa a kan hakan hukuma za ta bi masa kadi.''
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Justin Fashanu shi ne dan wasan kwallon kafa na farko a Ingila da ya fito fili ya bayyana cewa shi dan luwadi ne a1990, amma kuma y kashe kansa yana shekara 37 a 1998.
Tun daga wannan lokacin ba wani dan wasa kwararre da yake wasa a Ingila, da ya fito ya bayyana cewa shi mai neman jinsi daya ne.
Tsohon dan wasan Jamus da Aston Villa Thomas Hitzlsperger, shi ne ya zama na farko da ya yi wasa a Premier, wanda ya fito fili ya ce shi dan luwadi ne, a watan Janairu na 2014, bayan ya gama wasa a Ingila.
Tsohuwar kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ingila ta mata Casey Stoney, ita ce 'yar wasan kwallon kafa da ke wasa da ta fito fili a Ingila, tun bayan Fashanu ta bayyana cewa ita mai neman jinsinta ce, a watan Fabrairu na 2014.
A watan Oktoba wani bincike da BBC ta yi, ya gano cewa kashi 82 cin dari na magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa ba su damu ba idan kungiyarsu ta sayo dan wasa dan luwadi.
Sai dai kuma kashi takwas cikin dari na magoya bayan sun ce za su daina zuwa kallon wasan kungiyarsu, idan ta dauki dan luwadi.