An ci tarar Chelsea da Man City

Fernandinho yana cakumar Fabregas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kori Fernandinho saboda cakumar Cesc Fabregas da ya yi

An ci tarar Chelsea fan dubu 100 yayin da Manchester City za ta biya tarar fan 35,000 sakamakon rikicin da 'yan wasansu suka yi a gasar Premier a Etihad a farkon watan nan.

An samu hatsaniya ne tsakanin 'yan wasan bayan da Chelsea ta yi nasara 3-1, lokacin da alkalin wasa ya kori Sergio Aguero na City kan ketar da ya yi wa David Luiz.

Shi ma abokin wasan Aguero, Fernandinho alkalin wasan ya kore shi bayan da ya cakumi Cesc Fabregas lokacin da 'yan wasan kungiyoyin biyu ke hatsaniya.

Tun a baya hukumar kwallon Ingila ta gargadi Chelsea cewa idan ba ta yi hankali ba za a kai ga yi mata hukuncin rage mata maki.

Chelsean wadda ke jagorantar teburin Premier da wannan an yi mata hukuncin tara sau shida tun watan Fabrairu na 2015 saboda ta kasa tsawatarwa 'yan wasanta.

An ci tarar Chelsea fan dubu 375, wadda kuma aka rage zuwa dubu 290 bayan ta daukaka kara a sanadin hatsaniyar 'yan wasanta a haduwarsu da Tottenham a watan Mayu.

Daga nan ne hukumar kwallon kafa ta Ingila ta gargade ta cewa nan ba da dadewa ba za a kai ga yi mata hukuncin rage maki.

Sai dai kocin kungiyar Antonio Conte ya basar da maganar a wata hira da 'yan jarida suka yi da shi ranar Lahadi kan ko ba ya ganin matakin zai kai ga nakasta matsayin kungiyarsa a tebur, inda ya ce musu ko da gaske suke an yi wannan magana.

Manyan kungiyoyi biyu da aka taba yi musu hukuncin rage maki su ne Manchester United da Arsenal, a sakamakon rikicin da suka yi a Old Trafford a watan Oktoba na 1990.

Bayan wasan kocin Manchester City Pep Guardiola ya bayar da hakuri a kan abin da 'yan wasan nasa suka yi.

Aguero, wanda korar da alkalin wasa ya yi masa ita ce ta biyu a bana, an dakatar da shi wasa hudu yayin da aka haramta wa Fernandinho wasa uku.