Boko Haram: USAID za ta bayar da dala miliyan 92

Buhuhunan abinci da USAID ke bayar wa ga marasa galihu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

USAID ta ce za a yi amfanin da kudaden ne wajen samar musu da ababen more rayuwa, kamar abinci

Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa za ta bayar da gudunmuwar karin dala miliyan 92 ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a arewa-maso-gabashin Najeriya, da kuma yankin Tafkin Chadi.

Wannan dai ya biyo ne bayan gargadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi cewa mutane kimanin dubu 120 na cikin kasadar mutuwa saboda yunwa a shiyar ta arewa maso gabashin Najeriya sakamakon fadan aka a can.

Wata sanarwa daga Hedikwatar hukumar raya kasashe ta gwamnatin Amurkar wato USAID ta ce kudaden, wadanda za a rarraba ga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kungiyoyi zaman kansu da ke bayar da agaji a shiyyar, za a yi amfani da su wajen kai dauki ga dubban mutanen da ke bukatar agaji da gaggawa.

USAID ta ce za a yi amfanin da kudaden ne wajen samar musu da ababen more rayuwa, kamar abinci da ruwa da matsuguni da kuma wasu ayyuka, da ba su kariya.

A cewar sanarwar wannan ne ya kawo jimillar kudaden da gwamnatin kasar ta Amurka ta bayar a bana don taimakawa wadanda rikicin na Boko Haram da wasu bala'oi makamantansa suka shafa zuwa dala miliyan 291.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rikicin Boko Haram ya raba mutane da dama da muhallansu a Najeriya da shauran kasashe da ke makwabtaka

Rikicin dai ya jefa mutane kusan miliyan shidda da rabin cikin bukatar agajin abinci na gaggawa a kasashen Nigeria da Niger da kuma Chadi, kazalika ya raba mutane fiye da miliyan biyu da rabi da gidajensu da garuruwansu.

Sai dai wannan na zuwa a yayin da ake ci gaba da samun zargin da ake yi na karkata akalar kudade da kayan agaji da gwamnatoci da kungiyoyi a Najeriya ke bayarwa don tallafawa 'yan gudun hijirar.

A makon jiya ma majalisar dattawan kasar ta bude wani zaman sauraron koke-koken jama'a kan yadda ake karkata akalar kayan agajin.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, ana bukatar wasu kudi har dala biliyan 1 domin bai wa mutanen irin tallafin da suke bukata a shekara mai kamawa ta 2017.